Wani sabon fada ya barke tsakanin jami'an tsaron Armenia da Azerbaijan akan iyakokin kasashen biyu wanda bayanai ke cewa tarin dakarun Azerbaijan sun rasa ...
Ma’aikatar tsaron wadda ba ta sanar da irin illar da hare-haren ya yi mat aba ko kuma yawan dakarunta da suka rasa rayukansu, ta ce Azerbaijan ta yi amfani da jirage marasa matuka wajen kaddamar da wasu hare-hare a cikin Armenia. Ma’aikatar tsaron Armenia ta ce da sanyin safiyar yau talata ne, Azerbaijan ta kaddamar da hare-hare da makaman atillery kan dakarunta da ke biranen Goris da Sotk da kuma Jermuk. Wani sabon fada ya barke tsakanin jami’an tsaron Armenia da Azerbaijan akan iyakokin kasashen biyu wanda bayanai ke cewa tarin dakarun Azerbaijan sun rasa rayukansu a gwabzawar.
Armenia da Azerbaijan sun zargi juna da tsokano rikicin da ya barke a kan iyakarsu, wanda yayi sanadin mutuwar sojoji kusan 100 a baya bayan nan, ...
Da fari dai Azerbeijan ba ta bayyana adadin hasarar sojojin da tayi ba, amma daga baya a jiya Talata, ma'aikatar tsaron kasar ta Azerbaijan ta ce dakarunta 50 ne suka mutu a arangamar da suka yi da na Armenia cikin dare. Ma'aikatar tsaron kasar Armenia ta ce fadan ya barke ne da sanyin safiyar Talata lokacin da sojojin Azerbaijan suka kai hare-haren da suka halaka sojojin Armenia akalla 49, lamarin da ya tilasta musu mayar da martani. Armenia da Azerbaijan sun zargi juna da tsokano rikicin da ya barke a kan iyakarsu, wanda yayi sanadin mutuwar sojoji kusan 100 a baya bayan nan, fada mafi muni da aka yi tsakanin kasashen makwabtan juna, tun bayan yakin shekarar 2020 kan yankin Nagorno-Karabakh da su ke takaddama a kai.